An bukaci kasashen Africa suyi hattara da rikicin Darfur | Labarai | DW | 15.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci kasashen Africa suyi hattara da rikicin Darfur

Shugaban kungiyyar hadin kann kasashen Africa, Denis Sassou Nguesso yace dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na Mdd ne, a yanzu zasu ci gaba da tabbatar da tsaro, a iyakar kasashen Sudan da kuma Chad.

Daukar wannan mataki dai a cewar bayanai, ya biyo bayan ci gaba da rura wutar rikici ne dake faruwa ,a iyakar kasashen biyu daga bangaren yan tawaye.

Shugaban kungiyyar ta Au, ya kuma yi gargadin cewa matukar ba´ayi hankali ba, to babu shakka, rikicin yankin darfur ka iya shafar wasu kasashe na Africa.

Mr Denis Sassaou Nguesso yayi wannan gargadin ne kuwa jim kadan bayan ganawar sa da shugaba Jacques Chirac na faransa.

Bayanai dai ya zuwa yanzu sun shaidar da cewa har yanzu tana kasa tana dabo ,a game da kokarin zuwan dakarun Mdd izuwa yankin na darfur.