An bukaci kare rayukan bakar fata a Amirka | Labarai | DW | 29.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci kare rayukan bakar fata a Amirka

Shugabar hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta bukaci gwamnatin Amirka ta haramtawa 'yan sanda kashe 'yan kasar bakar fata.

Wannan kira ya biyo bayan barkewar zanga-zanga a Minneapolis, sakamakon mutuwar wani bakar fata mai suna George Floyd bayan shakewar da wani 'dan sanda farar fata ya yi masa. Bachelet ta kuma kara da bayyana wannan mummunan al'amari a matsayin guda cikin adadin Amirkawa bakar fata da suka rasa rayukansu a hannun jami'an tsaro ko kuma al'ummar kasar ta Amirka farar fata.

Michelle Bachelet wacce ta kasance tsohuwar shugabar kasar Chile ta jaddada muhimmancin sauya hanyoyin da 'yan sanda ke amfani da su wajen cafke masu laifi bayan ta bukaci a dinga gurfanar da jami'an tsaron da suka wuce makadi da rawa yayin gudanar da aiki. Hukumar kare hakkin dan Adam din ta Majalisar Dinkin Duniya ta ja hankalin masu zanga-zangar su guji tarzomar da za ta haifar da asarar dukiyoyi.