1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci hukunci mai tsanani kan jagororin zanga-zanga

Ramatu Garba Baba
January 8, 2018

Wani babban jami'i a ma'aikatar shari'a a Iran ya bukaci a aiwatar da hukunci mai tsanani kan jagororin da suka shirya zanga-zangar adawa da gwamnati da ya kasance mafi muni tun shekarar 2009.

https://p.dw.com/p/2qVQl
Iran Demonstration für die Regierung in Teheran
Hoto: Getty Images/AFP/A. Kenare

Hamid Shahriari ya fadi hakan ne a wata tattaunawar da ya yi da kafar yada labaran kasar inda ya jadadda bukatar aiwatar da hukunci kan jagororin da ke ikirarin samun sauyi a gangami kan adawa da gwamnati duk da cewa bai yi karin haske kan irin hukunci da ke jiran wadanda ake kallo da laifin cin amanar kasa dama yawan mutanen da aka kama a zanga-zangar ba. Iran ta yi kaurin suna wajen aiwatar da hukunci mai tsanani kamar kisa kan wadanda suka aikata laifi na cin amanar kasa. Rahotannin na cewa mutane fiye da dubu daya aka kama tare da tsare su a yayin zanga-zangar da ta balle na adawa da gwamnati kan tsananin rayuwa da rashin aikin yi kafin ta rikide zuwa ta neman sauyin gwamnati.