An bukaci da a kwashe Musulmin Bangui | Labarai | DW | 02.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci da a kwashe Musulmin Bangui

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a kwashe musulmin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da ke zaune a birnin Bangui da sauran birane saboda irin hare-haren da suke fuskanta.

Wannan kiran dai na zuwa ne daidai lokacin da shugabannin kasasashen Afrika za su yi wata ganawa a yau domin duba halin da ake ciki a Jamhuriyar ta Afrika ta tsakiya.

Cecile Pouilly jami'a ce a hukumar kare hakkin bani Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce irin yadda rikici tsakanin 'yan anti-Balaka da Musulmi ke jawo zub da jini ne ya sa suka ga dacewar bada shawarar debe musulmi daga kasar.

Ms Pouilly ta ce jerin arangama tsakanin 'yan anti-Balaka da Musulmi sun faru a yankuna da dama na babban birnin kasar a 'yan makonnin da suka gabata. A ranar 27 na watan da ya wuce an kashe mutane 20 da jikkata wasu sha daya bayan an kai harin gurneti kan masu jana'iza a unguwar PK5. A ranar 22 da 23 ga watan na jiya dai 'yan anti-Balaka sun afakwa unguwar ta PK5 inda ake zaton kimanin Musulmi 700 na makale.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu