An bukaci a kakaba wa Iran takunkumi | Labarai | DW | 02.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci a kakaba wa Iran takunkumi

Manyan kasashen duniya hudu sun bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki mataki a kan kasar Iran bisa sabon gwajin makami mai linzami da kasar ta yi.

Manyan kasashen duniya hudu sun bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki mataki a kan kasar Iran bisa sabon gwajin makami mai linzami da kasar ta yi. Faransa da Birtaniya da Jamus dama Amirka ne suka bukaci a dauki wannan matakin kamar yadda ya ke kunshe a wata wasikar da suka aikawa kwamitin, kasashen hudu sun kuma bukaci Iran da ta dakatar da gwajin tare da yin kira ga babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gueteress da kada ya bata wani lokaci wajen shigar da koken a gaban kwamitin.

Shirin kasar ta Iran na gwajin makami mai linzami, abu ne da ya saba wa dokar Majalisar Dinkin duniya, duk da cewa kasar ta sha musanta zargin take dokokin kasa da kasa. a farkon wannan shekarar ma Amirka ta kakabawa Iran wasu jerin takunkuman ladabtar da ita a kan gwajin makamin mai linzami da Amirkar ta ce tamkar goyon baya ne ga ta'addanci.