An bude taron neman tsagaita wutar rikicin Ukraine | Labarai | DW | 05.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron neman tsagaita wutar rikicin Ukraine

A birnin Minsk na kasar Belarussia wakilan tuntubar juna kan rikicin Ukraine sun fara taro yayin da ake gwabza fada a gabashin kasar.

Wakilan tuntubar juna a kan Ukraine sun fara tattauna batun kawo karshe rikicin yankin. Wakilan kasar Rasha da na gwamnatin Ukraine da kuma na kungiyar tsaro da hadin kai a Turai tare da na 'yan aware suna gudanar da shawarwari a Minsk babban birnin kasar Belarussia a kokarin cimma shirin tsagaita wuta a rikicin gabashin Ukraine. Sai dai rahotanni na cewa duk da fara wannan taro, har yanzu ba a kai ga tsagaita wuta ba, inda a can gabashin Ukraine din ake ci gaba da gumurzu tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan aware magoya bayan Rasha. Har yanzu kuma ana cikin halin rashin tabbas a Mariupol. Bayan da 'yan tawaye suka sanar da kame birnin, an jiyo kakakin rundunar sojin Ukraine na musanta wannan ikirari, yana cewa har yanzu birnin na hannun dakarun gwamnati.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo