An bude taron makamashi a birnin Berlin | Labarai | DW | 03.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron makamashi a birnin Berlin

A yau aka bude babban taron makamashi a birnin Berlin bisa jagorancin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Mahalarta taron waɗanda suka haɗa da manyan shugabannin kamfanoni da jamián kula da muhalli na nazari domin shawarta tabbatacciyar makoma ga matsalar makamashi a nahiyar turai, wanda zai rage dogaro ta samun makamashin daga yankin gabas ta tsakiya da kuma ƙasar Rasha, bugu da kari taron zai kuma yi muhawara domin warware sabanin da ake da ita ta fuskar makamashin nukiliya. Ana sa ran Angela Merkel za ta gana da shugabannin kamfanonin mai domin shawarta wani jadawali da zai zama matakin farko na samar da ƙwaƙwaran shirin makamashi nan da shekara ta 2010.