An bude rumfunan zabe a kasar Ruwanda | Labarai | DW | 04.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude rumfunan zabe a kasar Ruwanda

A wannan Juma'a ce 'yan kasar Ruwanda akalla miliyan shida da dubu 900 ke kada kuri'un su a zaben shugaban kasar inda Shugaba Paul Kagame ke neman wani sabon wa'adin mulki ne na uku na shekaru bakwai.

Mutumen da wasu ke masu kallon mai hangen nesa, yayin da wasu ke masa kallon dan kama karya, Kagame mai shekaru 59 da haihuwa, na fuskantar 'yan takara biyu, sai dai kuma mutane ne da 'yan kasar ta Ruwanda ba su san su ba sosai, kuma ba su yi wani tasiri ba yayin yakin neman zaben da ya gudana na tsawon makonni uku a kasar, inda babbar jam'iyya mai mulki ta FPR "Front patriotique Rwandais" ta baje kolinta.

Miliyoyin mutane ne dai suka tarbi shugaba Kagame tare da jinjina masa yayin wani babban taron gangami na karshe da ya jagoranta a ranar Laraba da ta gabata a Kigali babban birnin kasar. Dauke da tutar jam'iyyar mai launin ja da fari da bula magoya bayan shugaban sun sha alwashin sake mayar da shi a kan kujerarsa. Wani da aka yi hira da shi ya ce zai sake zaben Kagame ne, domin shi ne ya dagakatar da kisan kare dangi na 1994, sannan kuma ya kawo babban ci gaba a Ruwanda.