An buɗe zaman binciken harin Jirgin Gaza | Labarai | DW | 28.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An buɗe zaman binciken harin Jirgin Gaza

Turkiya ta janye Jakadanta a Tel Aviv da kuma hana Jiragen sojin Isra'ila amfani da sararin samaniyarta.

default

Sojojin Isra'ila a cikin Jirgin ruwan agajin Gaza

Shugaban kwamitin binciken harin da sojojin Isra'ila suka kai akan wani jirgin ruwan agaji ga al'uman Gaza ya ce za'a gaiyaci Firaminista da ministan tsaro na Isra'ila da su ba da sheda a gaban kwamitin binciken da aka kafa.

Tsohon alƙalin kotun ƙoli, Jacob Turkel, da ke jagorantar kwamitin da gwamnatin Isra'ila ta kafa, ya ce dole ne manyan jami'an gwamnatin su gurfana a gabansa domin sanin haƙiƙanin abun da ya kai ga sojojin na Israila kashe wasu Turkawa 8 da Ba'amirke guda da ke wannan jirgin ruwa.

Harin dai ya haifar da tofin Allah tsine daga ƙasashen duniya, ya kuma kai ga Turkiya ta janye jakadanta a Tel Aviv da kuma hana Jiragen sojin Isra'ila amfani da sararin samaniyarta.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balarabe Abbas