An buɗe taron ƙasa da ƙasa a Katar a kan canjin yanayi | Labarai | DW | 26.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An buɗe taron ƙasa da ƙasa a Katar a kan canjin yanayi

Tun lokacin da aka cimma wata yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa a kan batun cancin yanayi a ƙasar Japan, babu dai wani takamaiman sauyi da aka samu a kan batun.

default

Mahalarta taron Doha na kasar Qatar

Kimanin ƙasashen duniya 200 ne ake sa ran zuwan su a birnin Doha na ƙasar Ƙatar inda za su share makonni biyu su na tautaunawa a dangane da batun canjin yanayi a duniya. Shekaru 15 bayan wata yarjejeniyar da ƙasashen duniya suka sa wa hannu a ƙasar Japan da aka fi sani da sunan yarjejeniyar Kyoto, kawo yanzu dai babu wani sauyin da aka gani daga manyan ƙasashen da suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar. Duk da yake a shekara ta 1997 a ƙalla ƙasashe 40 ne suka amunce da rage budada hayakin gubar da suke sarrafawa daga kamfanoninsu a shekara, ta nan da wannan shekara ta 2012 , kawo yanzu babu wani takamaiman ci-gaban da aka samu daga ƙasashen.
Dama tun can farko ƙasar China ta bi sahun ƙasar Amurka gurin kin amuncewa da sa hannu a wannan yarjejeniyar. Yanzu haka masu lura da al'amura na ganin ko yanzu babu wani abun da za a cimma muddun ƙasasehn biyu har da Kanada ba su ɗauki nauyin da ya rataya a kansu ba a matsayinsu na manyan ƙasashen duniya.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal