1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗa taron NATO a birnin Lisabon na ƙasar Portugal

November 19, 2010

Shugabanin ƙasashe membobin Ƙungiyar tsaro ta NATO sun fara tattana batutuwan da su ka shafi harakokin gudanarwar Ƙungiyar.

https://p.dw.com/p/QDXA
Taron NATO a LisabonHoto: DW

Shugabannin ƙasashen ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO sun hallara a birnin Lisbon na ƙasar Portugal a taron ƙoli na ƙungiyar da aka soma a yau.

Taron wanda za a kwashe kwanaki biyu ana tattauna a ƙarshe ana sa ran shugabanin ƙasashen guda 28 za su amince da mahimman shawarwari waɗandada su ka haɗa da kawo sauye-sauye ga rundunar tsaron nan gaba a cikin shekaru masu zuwa, tare kuma da duba hanyoyin  janye bradan ƙungiyar  daga ƙasar Afganistan kafin ƙarshen shekara ta 2014 lokacin da za su mayar da al´amuran tsaro ga sojojin na Afganistan.

Ministan tsaro na ƙasar Jamus KARL Theodor zu Guttenberg ya shaida cewa janye sojojin Ƙungiyar daga Afganistan zai zama wata hanyar saki ga sojojin ƙungiyar:

Ya ce a ra'ayinsa, wannan wata dama ce ta kawo ƙarhen barazana da sojojinsu ke fama da ita a Afganistan kuma a ƙalla kafin nan da shekara ta 2014 za su iya cimma mafufofinsu.

Mawallafi: Abdurahman Hassane

Edita: Yahouza Sadissou Madobi