An bayyana sunaye wanda Buhari zai nada ministoci | Siyasa | DW | 06.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An bayyana sunaye wanda Buhari zai nada ministoci

Shugaban majalisar datawan Najeriya Bukola Saraki ya karanta sunayen mutane 21 da shugaban Najeriya ya ake son ya nada a mukamin minoistoci, batun da ya kawo karshen dogon jiran da al'ummar kasar suka yi.

A zaman majalisar na yau ne aka bayyana sunayen wanda za a nada ministocin wanda suka hada da Sanata Hadi Siriki daga jihar Katsina, da Janar Abdulrahman Dambazau daga Kano sai kuma Sanata Aisha Jummai Alhassan daga Jihar Taraba da Abubakar Malami daga jihar Kebbi da kuma shugaban kamfanin mai na kasar Emmanuel Ibe Kachukwu.

Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya ce za tantance ministocin a makon gobe.

Sauran sun hada da Babatunde Raji Fashola tsohon gwamman jihar Lagos da Dr. Ogbunaya Onu, da Solomon Dalong da kuma Chris Ngige. Akwai kuma Cif Audu Ogbeh da Ahmed Isa Ibeto tsohon mataimakin gwamnan jihar Niger da Kayode Fayemi da kuma Amina Ibrahim.

Tuni dai 'yan majalisar dattawan Najeriya ta Najeriya suka sanar da cewar za ta bi hanyoyin da suka dace wajen tantance ministocin kuma za ta yi aikin ne ba sani ba sabo kana za su tantance su ne ba cikin kankanin lokaci don ganin sun kama aiki da nufin ciyar da kasar gaba.

Tuni dai 'yan Najeriya suka fara fadin albarkacin bakunanasu kan sunayen mutanen da aka mika musamman ma da ya ke wasu da aka gabatar sanannu ne, batun da ya sanya aza ayar tambaya ta sauyin da aka sa ran za ci gani. Wannan dai ya sanya Abdulrahman Kawu Sumaila mai baiwa shugaban Najeriya shawara a fanin majalisar wakilai cewa ''babu wani mutum komai tsarkinsa da mutane ba za su yi magana a kansa ba, duk wanda yake da korafi sai ya kawo a duba''

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria

Majalisar dattawa ta ce za ta bi matakan da doka ta tanada wajen tantance ministoci.

Majalisar dai ta tsayar da ranar 13 ga watan da muke ciki domin fara tantance mutanen da za a nada mukamin ministoci a kasar, yayinda ake sa idon ganin shugaban ya aiko da sauran mutane goma sha biyar din da su ma za a tantace kafin a nada ministoci kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar shaida. 'Yan Najeriya dai yanzu haka na sa ido don ganin kamun ludayin 'yan majaliasar wajen wannan aiki na tantancewa.

Sauti da bidiyo akan labarin