An bayyana ƙauyen Bili´in da zama nasara adawa da katangar Isra´ila | Labarai | DW | 04.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bayyana ƙauyen Bili´in da zama nasara adawa da katangar Isra´ila

Mazauna kauyen Bili´in dake Gabar yamma da Kogin Jordan sun yi maraba da hukuncin da kotun kolin Isra´ila ta yanke wanda ya umraci Isra´ila da ta canza hanyar ganuwar nan da take ginawa a wannan yanki. Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta saurari karar da Falasdinawa suka shigar cewa katangar ta ratsa kan gonakin su kuma hakan zai zasu shiga cikin halin ni ´yasu. Jim kadan bayan sanar da hukuncin kotun mazauna kauye sun bazu kan tituna suna nuna farin cikin su.

Masharhanta sun bayyana kauyen na Bili´in da cewa wata alamar nasara ce ga adawar da Falasdinawa ke nunawa gina ganuwar.