An ba da kyautar Nobel ta kimiyya | Labarai | DW | 04.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ba da kyautar Nobel ta kimiyya

Wasu 'yan kasar Birtaniya ne guda suka samu kyautar saboda gudunmowar da suka ba da ta fannin inganta al'amuran latronik.

An ba da kyautar Nobel ta kimiyya ga wasu 'yan kasar Birtaniya guda uku wadanda ke yin aikin bincike a Amirka.David Thouless da Duncan Haldane da kuma Michael Kosterlitz,sun samu kyautar saboda bincike da suka gudanar a game da samar da hanyoyin inganta sha'anin latronik ta hanyar lisafi mai surfi.Cibiyar Nobel Fondation da ta ba da  kyautar a birnin Stockholm ta ce bincike  ya taimaka sossai wajen samun ci gaba a game da sha'anin latronik da sauran abubuwa na kimiyya.