An aiwatar da hukuncin kisa ga mutun hudu a Saudiyya | Labarai | DW | 17.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An aiwatar da hukuncin kisa ga mutun hudu a Saudiyya

Hukumomi a kasar Saudiyya sun zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane hudu ta hanyar fille musu kanu, bayan da aka kamasu da laifin kisan kai a kasar.

Rahotanni daga birnin Riyad na kasar Saudiyya na cewa, an aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar fille kanu ga wasu mutane guda hudu a kasar, da suka hada da 'yan kasar Sirilanka mutun uku, da wani dan kasar Masar daya bayan kamasu da laifin kisan kai a cewar ofishin ministan cikin gidan kasar ta Saudiyya. 'Yan kasar ta Sri-Lanka guda uku an kama su ne da laifin kashe wani dan kasar Saudiyya ta hanyar toshe masa kafofin nunfashi yayin da suka je sata gidansa, kuma an kashe su ne a birnin Jiddah.

Daga farkon bana dai kawo yanzu an aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar fille kanu ga mutane a kalla 120 a kasar ta Saudiyya, inda kisan kai, ko Fyade, da fashi da makami ko ridda ke da hukuncin kisa a wannan kasa kamar yadda dokar Muslunci ta tanada.