An ɗan samu ci-gaba a kan muradun ƙarni | Zamantakewa | DW | 09.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An ɗan samu ci-gaba a kan muradun ƙarni

Wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana a kan maradun ƙarni na nuna cewar an samu ci-gaba, sai dai har yanzu da sauran aiki a kan maganar yaƙi da yunwa da kuma talauci.

A fannin kiwon lafiya Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an samu ci-gaba mai ma'ana wajen yaƙi da cututtukan zazzaɓin cizon sauro da tarin fuka. Wanda ta ce an kaucewa mutuwar mutane sama da miliyan uku daga shekarun 2000 zuwa 2012 daga kamuwa da cutar , galibi yara ƙanana saboda gidajen sange da aka ba da ga iyalai kyauta.

A kan yaƙi da talauci babu wani sauyi da aka samu

Menschen aus Uganda Bilder aus Kampala Flash-Galerie

Dangane da abin da ya sahfi yaƙi da yuwan da talauci ƙasashe 193 suka cimma manufofin tun a shekarun 2000, sai dai a cikin ƙasashe masu tasowa har yanzu kashi ɗaya bisa biyar na al'ummar ƙasar na yin rayuwa da ƙasa da dala Amirka ɗaya a yini. Barbara Unmüßig wata ƙwararra ce ta wata cibiya da ke kula da yanyi da kuma ci gaba a nan Jamus wato Henrich Boll.

''Idan da arzikin ma'addanai da ake da shi a nahiyar Afirka ribarsa al'umma na amfana da ita , to kam da an rage talaucin kuma dama ba sai an riƙa bai wa ƙasashen ba taimako raya ƙasa.''

Ci-gaba a kan sha'anin ba da ilimi, duk da ƙalubalen da ake fuskanta

MDG Indien Bildung 2

Rahoton ya ce yara kimanin miliyan 58 'yan shekaru shida zuwa 11 na fama da rashin samun ilimi a duniya, wadanda ba sa zuwa makaranta, sai dai duk da haka an ɗan samu ci-gaba tun daga shekarun 2007. Sannan an samu sauyi a cikin ƙasashe 17 a tsawon shekaru gomai waɗanda suka rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kashi 90 cikin ɗari.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman