1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ɗage dokar ta ɓaci a kasar Philippines

March 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6C
Shugabar ƙasar Philippines Gloria Arroyo ta ɗage dokar ta bacin na tsawon mako guda da aka sanya a ƙasar bayan yunƙurin juyin mulki da aka zargi wasu jamián sojin ƙasar da aikatawa. Shugabar kasar Gloria Arroyo ta sanar da dage dokar ta bacin ne a jawabin da ta yiwa alúmar ƙasar bayan da masu bata shawarar a kann alámuran tsaro suka tabbatar mata da cewa komai ya lafa, babu wata fargaba ta juyin mulkin a yanzu. A halin da ake ciki, an tuhumi a kalla mutane 50 waɗanda suka haɗa da yan adawa da kuma jamián soji da yunƙurin kifar da gwamnatin