Amurka ta karawa Iran Takunkumi | Labarai | DW | 25.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta karawa Iran Takunkumi

Amurka ta kakaba takunkumi wa kimanin kamfanonin Iran 20 ,da manyan bankuna da fitattun yan kasar dama maaikatar tsaron ta.Wannan na bangaren matakan da Amurkan ta dauka domin matsin lamba wa Tehran,na watsi da shirin nucleanrta,kamar yadda sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta bayyana…….

„Hakan na nufin cewar ba bu wani BaAmurke ko kungiya mai zaman kanta,da zaa aminewa ya shiga wata huldar kudi da waddannan mutane ko kuma hukumomi.Kazalika ,dukkan kaddarori da wadannan hukumomi da mutane suka mallaka,wadanda kuma ke Amurka,zaa dakatar dasu,ba tare da bata lokaci ba.Hakan zai taimaka wajen karetsarin kasa da kasa na wasu mu’amaloli na kudi da gwamnatin Iran“