1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta fice daga yarjejeniyar kula da 'yan gudun hijira

Zainab Mohammed Abubakar
December 3, 2017

A wani sako da ta yayata ta shafinta na Twitter jakadar Amurka a Majalisar Nikki Haley ta ce, daga yanzu Amurkawa su kadai ne za su iya zartar da kowane hukunci da ya danganci 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2ogE0
USA UN-Sicherheitsrat Nikki Haley
Hoto: Getty Images/D. Angerer

Yarjejeniyar kasa ta kasa da aka cimma a watan Satumban 2016, na da nufin karfafa yadda za'a kula da lamuran 'yan gudun hijirar a duniya baki daya, kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta MDD ta nunar.

Kazalika yarjejeniyar na da nufin samar da shiri na bai daya, ta yadda kasashe za su tabbatar da kare martabar 'yan gudun hijirar da duk wani nau'i na tozartawa da nuna wariya daga al'umma.

Sai dai a cewar jakadar Amurka Haley, tanadin yarjejeniyar wanda kasashen da suka rattaba hannu ke shirin fara aiwatarwa a shekara ta 2018 mai kamawa, bai dace da akidojin Amurka ba.