1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta dora wa jagororin Sudan takunkumai

June 2, 2023

Gwamnatin Amurka ta sanar da matakin kakaba takunkumai a kan jagorori masu gaba da juna a Sudan, saboda barazanar da suke yi wa zaman lafiya da tsaro da ma daidaito.

https://p.dw.com/p/4S69q
Hoto: Hanna Johre/NTB/REUTERS

Sakataren harkokin wajen Amurkar Anthony Blinken ya sanar da cewa matakin kakaba takunkuman wani kashedi ne kan aika-aikar da sojojin Sudan da ma mayakan rundunar kar ta kwana na RSF ke aikatawa da ke kuntata wa rayuwar 'yan Sudan da ma dimukuradiyya.

Daga cikin abin da takunkuman suka kunsa, har da hana duk wani wanda ke da hannu a rikicin Sudan din izinin shiga Amurka da ma wasu wadanda za su durkusar da harkokin tattalin arziki.

Cikin watan jiya ne dai wakilan bangarorin da ke rikici a Sudan suka yi zama a Saudiyya inda suka amince da tsagaita wuta tare da kare fararen hula, amma kuma daga bisani aka ci gaba da kai wa juna hare-hare.

Amurkar dai ta ce a shirye take ta tsara tare da gabatar da wasu karin matakai a kan jagororin na Sudan.