Amurka na shirin janye sojojinta daga Afghanistan | Labarai | DW | 12.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka na shirin janye sojojinta daga Afghanistan

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi gargaɗin cewar a cikin watannin ukku masu zuwa aikin sojojin Amurka da na NATO a Afganistan zai kasance na bayar da tallafi.

Obama ya baiyana haka ne a a taron manema labarai da ya kira jim kaɗan bayan da ya gana da shugaban ƙasar na Afganistan Hamid Karzai wanda ya kammala ziyara aiki a Amurkan. Ta na da sojojin kusan dubu 68 a Afghanistan. Kuma ana saran kafin nan da ƙarshen shekara ta 2014 lokacin da za a kwashe su baki ɗaya, za a rage yawan dakarun ƙasashen duniyar da sannun a hankali, wani mataki na mayar da ragamar tsaro ga sojojin ƙasar. Kana shugaba Hamid Karzai ya yi marhabin da kafa wata cibiya da aka yi a birnin Doha na ƙasar Qatar domin fara tattaunawa tsakanin gwamntinsa da ƙungiyar taliban.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Mouhamadou Awal