Amurka da rikicin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 10.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka da rikicin nukiliyar Iran

Shugaban Amurka George W Bush ya baiyana alámarin kasar Iran da cewa batu ne mai matukar damuwa ta fuskar tsaro. Bush yace ya son ganin an sami hanyar diplomasiyya ta warware takaddamar nukiliyar ta kasar Iran. Shugaba George W Bus yace Amurka ta damu musamman da kudirin Iran na ganin ta wargaza kasar Israila, sannan kuma Amurka ta yi Imani Iran na da burin mallakar makamin Nukiliya. Bush yace a saboda haka yana da matukar muhimmanci ga Amurka ta hada hannu da sauran kasashe domin warware wadannan matsaloli. Iran dai ta ce makamashin ta na nukiliya na lumana ne .