Amnesty ta zargi jamian tsaron Nigeria da cin zarafin mata | Zamantakewa | DW | 28.11.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Amnesty ta zargi jamian tsaron Nigeria da cin zarafin mata

default

Kungiyar kare hakkin jamaa ta kasa da kasa,watau Amnesty International,tayi kira ga hukumomin tarayyar Nigeria dasu gaggauta yiwa dokokin shariar kasar gyaran fuska ,domin rage karuwan tozartawa mata da jamian tsaro keyi,ta hanyar yi musu fyade.

A wani rahotan data gabatar mai shafuna 40 wanda tayiwa lakabi da sunan Fyade,makamin karkashin kasa,kungiyar ta Amnesty ta zargi karuwar batutuwan yiwa mata azaba ta hanyar fyade a bangaren jamian tsaron kasar ,da lalacin sashin sharia a Nigeria.

Duk da shekaru bakwai da zaban shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeriar akarkashin mulkin democradiyya,har yanzu sojojin kasar na cin moriyar kariya.

Directan kula da shiyyar Afrika na kungiyar Amnesty Kolawole Olaniyan ,yace abun ban tsoro shine, matan dakan fada irin wannan cin mutunci ,na fuskantar barazanar tsiratarwa a bangaren jamian yansanda,kana a bangaren gwamnati ,kuwa daman babu wani abunda zaayi na hukunta wadanda keda alhakin wannan cin zarafin.

Bugu da kari Bakin cikin da matar da akayiwa fyade zata kasance aciki,bashi da misaltuwa ,ga barazanar tsoratar da ita da jamian yansanda zasuyi,a wannan kasa da harkokin rashawa da rashin sanin kamun ludayi yayiwa katutu,inji Amnesty International.Kashi 10 dagha cikin 100 na yawan mata da ake cin zarafinsu ne kadai,ke samun nasara adangane da kararraki da suka shigar.

Rahotan kazalika ya bayyana yadda jamian tsaro a Nigeriar ke yiwa mata Fyade a gaban mazajensu na aure da yayan cikinsu,da yadda ake amfani da fasassaun kwalabe a farjin mata dake tsare a gidajen kurkuku.

Amnesty Int ta bada misalin yawan mata dake fadawa tarkon jamian tsaro ta hanyar fyade da wasu nauoi na azabtarwa,bisa ga kiyasin wata kungiya mai zaman kanta a kasar da ake kira Cleen Foundation,wadda tace akwai kimanin mata dubu 13,852 da akayiwa fyade da wasu cin mutunci dakwe da alaka da hakan,daga shekarata 1999-2005.

Adangane da hakane kungiyar tayi kira ga hukumomin Nigeriar dasu agazawa matan ta hanyar ceto su daga irin wannan cin zarafi da suke fuskanta daga jamian tsaro,musamman sojoji.

To sai dai kakakin Rundunar sojin Nigeria Colonel Ayo Olaniyan ,yace an wuce gona da iri adangane da wannan zargi.

 • Kwanan wata 28.11.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvT8
 • Kwanan wata 28.11.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvT8