1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta soki yarjejeniyar EU ta Turkiyya

Zainab Mohammed AbubakarJune 3, 2016

Kungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta yi kira ga Kungiyar Tarayyar Turai da ta dakatar da shirinta na mayar da 'yan gudun hijira da ke neman mafaka zuwa kasar Turkiyya.

https://p.dw.com/p/1IznK
Griechenland Idomeni Bahnhof mit Flüchtlingen und Zelten
Hoto: Reuters/M. Djurica

Kungiyar mai fafutukar kare hakkin al'umma ta yi wannan roko ne acikin wani bayani data gabatar mai shafuka 35, inda ta ce wannan mataki na Eu bai dace ba domin ya sabawa ka'ida.

A yanzu haka dai kasar Turkiyya na zama mai saukin 'yan gudun hijira miliyan 3, da suka hadar da 'yan Siriya 2.75, kuma tana saran samun karin wasu bisa ga yarjejeniyar da Turkiyyan ta cimma da Tarayyar Turai.

Yarjejeniyar dai ta tanadi cewar dukkan 'yan gudun hijira da suka isa tibirin Girka bayan ranar 20 ga watan Maris, za'a tusa keyarsu zuwa Turkiyya.

A madadain hakan, Turai zata karbi dan gudun hijirar Siriya guda daya daga Turkiyyan. Daura da haka, turkiyya zata ci moriyar kudi euro biliyan 6, tafiye tafiye ba tare da takardar izini ba, tare da gaggauta tattaunawar batun shigar da ita cikin Kungiyar Tarayyar Turai.