1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amnesty: Hukuncin kisa na karuwa a Masar

Ramatu Garba Baba
December 2, 2020

Kungiyar  Amnesty International ta baiyana damuwa kan yadda gwamnatin Masar ke ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa a yayin da ake son ganin an soke amfani da dokar a sauran sassan duniya.

https://p.dw.com/p/3m6Fa
Ägypten Todesurteil gegen Mohammed Badie ARCHIV
Hoto: picture-alliance/dpa/Str

Kungiyar  Amnesty International, ta soki gwamnatin kasar Masar bisa laifin aiwatar da hukuncin kisa da tayi kan gomman mutane a watanni biyu da suka gabata. A sanarwar da ta fitar, ta ce kusan mutum sittin aka kashe a tsakanin watannin Oktoba da Nuwambar da suka gabata, cikinsu har da mata, ana yanke musu hukuncin duk da tababan da ake kan laifukan da ake tuhumarsu.

Wani abun damuwa dai, shi ne yawan wadanda ake tsare da su yanzu a gidan yari, da su da iyalansu ba su da masaniya kan hukuncin da ke jiransu na kisa, mataki ne da ya tauye hakkin kowanne bil'adama injin´kungiyar. Lamarin ya fi shafar 'Yan jarida da masu fafutuka da lawyoyi da malaman jami'oi da 'yan siyasa da gwamnati ke zargi bisa laifuka na sukar muradun gwamnati.