Amnesty ta soki Jamus kan ′yan gudun hijira | Siyasa | DW | 25.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amnesty ta soki Jamus kan 'yan gudun hijira

A rahotonta na bana Kungiyar Amnesty International ta soki lamirin Jamus a dangane da manufofinta da suka shafi 'yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa a kasar

Kungiyar ta Amnesty International dai ta nuna matukar damuwa da abubuwan da ke faruwa a Jamus musamman karuwar abin da ta kira "aikata laifukan kyama" a kan 'yan gudun hijira da kuma manufofin gwamnatin Jamus da suka shafi masu neman mafakar siyasa a kasar. Selmin Caliskan ita ce babbar sakatariyar kungiyar ta kare hakkin dan Adam a Jamus ta yi karin haske.

Ta ce: "A shekarar 2015 masu neman mafaka kimanin miliyan daya ne suka shigo Jamus. Gwamnati ta ba da gagarumar gudunmawa inda ta nuna shirin taimakon wadannan mutane dda suka fito daga kasashe da yawa, kuma ke cikin halin ni 'ya su. Amma yawan kai hare-hare kan 'yan gudun hijira a Jamus ya dakushe wannan gudunmawa."

Deutschland Flüchtlinge in Berlin

Gadajan 'yan gudun hijira a Berlin

Selmin Caliskan ta ce a bara kawai hare-hare fiye da DUBU ne aka kai kan masu neman mafakar siyasa a Jamus, inda ta ba da misali da wani mummunan lamarin kyamar baki da ya auku kwanan nan a garuruwan Clausnitz da Bautzen da ke a jihar Saxony, to sai dai ta ce matsalar ba ta tsaya a wannan jiha ta gabashin Jamus kadai ba.

Ko da yake Amnesty ta yaba da yunkurin gwamnatin Jamus na karbar 'yan gudun hijirar da hannun bibiyu musamman ma kalaman shugabar gwamnati Angela Merkel a watan Satumban bara cewa Jamus za ta iya, a matsayin kyakkyawar alamar nuna wa 'yan gudun hijirar zumunci, amma abin takaici yanzu gwamnatin ce da kanta ta yi watsi da wannan mataki, inji Selmin Caliska.

Ta ce: "Gwamnatin tarayya ta yi fatali da matakin na yin haba-haba da 'yan gudun hijirar. Maimakon haka ana daukar tsauraran mataka ne na yin waje da su. Mun fahimci cewa an yi fatali da dokokin kariya na kasa da kasa."

Amnesty International PK zur Lage der Menschenrechte 2015/2016 Selmin Çaliskan

Babbar sakatariyar kungiyar Amnesty International Selmin Çaliskan

Kungiyar ta Amnesty ta kuma soki gwamnatin Jamus da sanya sunayen kasashen Aljeriya da Marokko da Tunisiya a jerin kasashe masu kwanciyar hankali. Amnesty ta ce kasashen guda uku sun yi kaurin suna wajen keta hakkin dan Adam. Wiebke Judith ita ce wakiliyar Amnesty International a Jamus da ke kula da batun kaura.

Ta ce: "Bugu da kari muna suka dangane da dokokin kotun kare kundin tsarin mulki musamman ka'idojin da kotun ke bi na ska sunan kasar da ke a kwanciyar hankali kuma bbau muzugunawa a cikinta. Amma a wadannan kasashe uku na arewacin Afirka ana fatali da hakkin tsiraru misali masu neman jinsi."

A wata sabuwa dai a wannan Alhamis din ce majalisar dokokin Jamus ta kada kuri'ar amincewa da sabuwar doka kan neman mafaka a kasar. Dokar dai ta tanadi gaggauta duba takardun masu neman mafaka da saukaka mayar da su kasshensu na asali, sai kuma kakkafa cibiyoyi na musamman na tsugunar da 'yan gudun hijira a fadin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin