1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta ce fursunoni na wahala a Najeriya

Pinado Abdu WabaSeptember 18, 2014

Bayan shekaru 10 tana bincike, kungiyar Amnesty International ta bayyana rahoton da ya gwada irin cin mutuncin da ake wa fursunoni a Najeriya

https://p.dw.com/p/1DF86
Nigeria Folteropfer Archiv 2013
Hoto: Amnesty International

Masu rajin kare hakkin bil adama sun ce ana cin zarafin fursunoni fiye da kima a gidajen yarin Najeriya. Kungiyar kare hakin bil adama ta Amnesty International ce ta bayyana hakan a wani rahoton da ta wallafa wanda ya kunshi bayyanai daga shaidun gani da ido da sauran hujjojin da ta dauki shekaru 10 tana tarawa dangane da wannan batu, abin da ya sa ta yi wa rahoton taken "Barka da zuwa wutar jiharnama - Cin zarafi da rashin kyautatawa a Najeriya". Kungiyar dai ta ce za ta gabatar da sakamakonta a biranen Abuja a Najeriya da Berlin a Jamus.

Wasu daga cikin abubuwan da ake zargin 'yan sanda da sojoji da aikatawa sun hada da cin zarafi ta hanyar lalata, mummunar duka, da amfani da lantarki dan jan mutane, da yanke yatsun hannu, da kunban kafa da hakora.

Duk wadanda aka daure dai ana hana su hulda da kowa daga waje, abin da ya hada da lauyoyi da yanuwa. A cewar rahoton na Amnesty, manufar yin hakan shi ne tilasta musu daukar alhakin laifin da ake zarginsu da shi, daga nan kuma a tilasta musu biyan kudi mai yawan gaske.