Amnesty ta ce an kashe yara kanana a Mosul | Labarai | DW | 22.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty ta ce an kashe yara kanana a Mosul

A cikin wani rahoton da ta baiyana Kungiyar kare hakin bil Adama ta Amnesty International ta ce, yara kanana da dama sun galabaita wasu ma an jikkatasu a yakin da ake yi a Iraki

Wata jami'ar kungiyar ta ce ta gana da wasu yaran wadanda suka sha azaba da arkane, yayin da wasu ma aka karkashesu a birnin na Mosul a yakin da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye. Muna wata matar da ta ba da shaidu a cikin rahoton ta ce, ta rasa ya'yanta 'yan mata guda biyu 'yan shekaru takwas da 14 a cikin barin wutar da ake yi ba dare ba rana a birnin na Mosul. Watanni biyu ke nan da suka wuce sojojin Iraki da ke samun goyon bayan kasashen duniya ke kokarin korar 'yan tawayen na IS daga Mosul.