Amnesty International ta zargi Mali da karya dokokin hakkin ɗan Adam | Labarai | DW | 21.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty International ta zargi Mali da karya dokokin hakkin ɗan Adam

Ƙungiyar ta zargi gwamnatin Malin da kule yara sojoji a kurkuku ba tare da barin iyalensu ba ko lauyoyinsu na kai musu ziyara.

Yaran waɗanda shekarun ba su kai ba shiga aikin soji gwamnatin na zarginsu da kansacewa mayaƙa na kungiyoyin da ke ɗauke da makamai ba bisa ƙaida ba.

Ƙungiyoyin mayaƙan masu fafutuka na yin amfani da yara ƙanana a matsayin soji a yaƙin da suke yi da gamnatin ƙasar Mali domin kafa daula ta musulunci tun a shekarun 2012 lokacin da yaƙi ya ɓarke a ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu