1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty: Hukuncin kisa ya ragu

April 10, 2019

A rahotonta na shekara kan hukuncin kisa kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty ta ce an samu raguwar zartar da hukuncin kisa a duniya da kashi 31 cikin 100.

https://p.dw.com/p/3GZJI
Gegen die Todesstrafe
Hoto: picture-alliance/W. Steinberg

A shekara ta 2018 mutane kimanin 690 aka yanke masu hukuncin kisa a cikin kasashe guda 20, yayin da a shekara ta 2017 aka samu har mutane 993. Kasashen da ke kan gaba a wajen yanke hukuncin kisan bayan Chaina su ne Iran da Saudiyya da Vietnam . Hakan kuwa na zuwa daidai lokacin da gwamnatin kasar Burunai ta amince da wata dokar ta yin kisa ta hanyar jefewa ga masu yin luwadi da madigo a karkashin wasu dokoki na tsarin shari'ar Musulunci.

Kungiyar ta Amnesty International ta ce an samu raguwar hukuncin kisan musamman a cikin kasashen da galibi ake aiwatar da hukuncin kisan misali Iran da Pakistan da Iraki wadanda suka yi sassauci ga hukunci a game da safarar miyagun kwayoyi. Hakan ya kara kwarin gwiwa a fafutukar da kungiyar ke yi na ganin an soke hukuncin kisan. Makwanni kadan kafin bayyana rahoton na shekara ta 2018. Sultan Hassanal Bolkiah na Kasar Burunai ya bayyana wani shirin kudirin doka na yanke hukuncin kisa ga masu yin luwadi da madigo da mazinata. Ravina Shamdasani ita ce kakakin kwamishinan kare hakin bil Adama a MDD ta ce sai da kwamitin kare hakin bil Adama na MDD ya yi kira ga sarkin Burunai da ya amince da wannan doka, ta ce wani hukunci ne mai tsanani da ba za a taba amincewa da shi ba.

Pakistan Proteste gegen Christin Asia Bibi
Asia Bibi daya ce daga cikin mutane da suka fuskanci barazanar kisa a Pakistan kamar yadda hoton nan ya nunarHoto: Getty Images/AFP/A. Hassan

Tun farko gwamnatin Jamus ta kira jakadan kasar Burunai a game da sabbin dokokin na tsarin shari'ar Musulunci da kasar ta tanada, yayin da yanzu haka 'yan luwadin da madIgo a yankin Kudu maso Gabashin Asiya ke fuskantar barazana.

Kusan shekaru 60 kungiyar ta Amnesty International ke yin gwagwarmayar ganin an soke hukuncin na kisa. A ranar 17 ga watan Disamba na shekara ta 2018 kasashe 121 cikin 193 suka amince da kudirin MDD na soke hukuncin kisan, yayin da 35 suka hau kujerar naki.

A lokacin da aka girka MDD a shekara ta 1945 kasashe takwas ne kawai cikin 51 suka soke hukuncin kisan yayin da a yau ake da sama da kasashe guda dari.