Antony Blinken zai kai ziyara kasar Habasha
March 10, 2023Talla
A mako mai zuwa, Sakataren Harkokin Wajen Amirka Antony Blinken zai gana da firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed da jagororin yankin Tigray a wata ziyarar aiki da zai kai yankin da ya sha fama da rikici. Ana sa ran ziyarar Blinken za ta taimaka wajen warware rikici a tsakanin bangarorin biyu da ke barazana ga kasar da ke yankin Kahon Afirka. An kwashi sama da shekara daya ana fada a tsakanin rundunar gwamnati da na 'yan tawayen TPLF, rikicin da ya yi sanadiyar salwantar daruruwan rayuka baya ga wasu kusan miliyan daya da suka rasa gidajensu.