Amirka za ta taimakawa matasan Afirka | BATUTUWA | DW | 21.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Amirka za ta taimakawa matasan Afirka

Amirka ta jaddada aniyarta ta taimakawa matasan nahiyar Afirka su samu ayyuka a cikin sababbin manufofin gwamnatin Shugaba Donald Trump na son yin hulda da kasashen nahiyar.

Karamin Sakatare kan huldar Amirka da nahiyar Afrika, Jakada Tibor Nagy ne ya bayyana haka cikin wani shirin amsa tambayoyi ta Internet da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta shirya a birnin Washington DC. Jakada Nagy wanda ya ce a ziyarar da ya kai kwanan nan a Afirka, ya yi tattaunawa mai tasiri da shugabannin gwamnatoci, da kungiyoyi dabam-dabam da ma shugabannin addini. Ya kuma yi tsokacin cewa sabuwar manufar, za ta kasance mai inganci sosai yana mai fatan matasan Afirka wadanda nan da shekara ta 2050 za su rubanya, za su rika damawa tare da yin gogayya kamar takwarorinsu na Amrika da Chaina da sauran nahiyoyi. Manufar Amrika dai shi ne, gwamnatocin Afrika su bude kofofinsu ga 'yan kasuwar Amrika su kuma rika nuna adalci wajen bayar da kwangila. 

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin