1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Amirka za ta janye wasu sojojinta

Ines Pohl MA/LMJ
July 30, 2020

A Larabar wannan makon gwamnatin Amirka ta sanar da shirinta na janye dakarunta dubu 11 da 900 daga cikin dubu 36 da take da su a Jamus.

https://p.dw.com/p/3gAvI
Donald Trump in Ramstein
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Craighead

Matakin gwamnatin Amirkan dai, na fuskantar suka daga kasashen Jamus da ma ita kanta Amirkan. Tun cikin watan Yunin da ya gabata ne dai Shugaba Donald Trumop na Amirkan, ya sanar da shirin janye wasu daga cikin dakarun kasarsa da ke Jamus, a daidai lokacin da ake musayar kalamai tsakanin Amirkan da Jamus dangane da kudin dawainiyar harkokin tsaro, wanda ya yi kasa da mizanin kashi biyu cikin 100 na kason da aka amince za a rika samar wa kungiyar tsaro ta NATO daga cikin kudin haraji na cikin gida. Kusan dakaru dubu 5,600 za a sake wa wurare a tsakanin kasashe mambobin kungiyar tsaron ta NATO, yayin da dubu 6,400 za su koma Amirka.

Amirka ta daina kare Jamus

Shugaba Trump dai ya tsaya kan cewa Jamus ce ta fi cin moriyar dakarun, duk da cewar suna tsare nahiyar Turai ne: "Suna can don aikin kare nahiyar Turai ne, suna can don kare Jamus ne kuma Jamus din ba ta biyan komai, abin kuma da ya kamata a ce tana yi ke nan. Don haka ina dalilin barin sojojin namu a can? Shekaru 25 ke nan da ake ta morar Amirka ta wannan bangare da ma harkokin cinikayya. Muna nan muna ta kare Jamus kawai."
Masana harkokin tsaro dai musamman a Amirkan, sun soma nuna damuwa kan wannan mataki na Shugaba Trump, inda wasunsu ke ganin dangataka tsakanin manyan kasashen biyu ka iya fuskantar matsala. Laftanar Janar Ben Hodges wani tsohon hafsan soja ne a Amirkan da ya taba jagorantar dakarunta a nahiyar Turai a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2017, a hirarsa da tashar DW cewa ya yi: "Yana yi mana ciwo, saboda mataki ne da zai kara lalata dangantaka tsakanin Amirka da muhimmiyar kawarta wato Jamus. Kamata ya yi in ma za a yi a dauki lokaci. Jamus na bamu damar tsara wasu dabarunmu na tsaro a kasashen Afirka da Turai da ma wasu kasashen Asiya. Kawa ce da Amirka ke bukata  fiye da kowace. Wannan gwamnatin dai na bin wannan tsari ne da a ganina, zai nakasa yardar da ke tsakaninmu."

Generalleutnant Ben Hodges
Tsohon tsohon hafsan sojan Amirka, Laftanar Janar Ben Hodges Hoto: picture-alliance/dpa/I. Wagner

Tsare Amirka ko kare Jamus?

Tsohon hafsan tsaro na Amirka dai na ganin dakaru dubu 35 da ake batu a kansu, ba su ma kai rabin 'yan kallon da suke shiga filin wasan kwallo don kallon 'yan wasan Bayern Munich ba. Kuma a cewarsa galibinsu ma'aikata ne da ke aiki a shelkwatocin da ke kula da ayyukan zirga-zirga da kuma fannonin sadarwa. Don haka ba wasu dakaru ne masu yawa ba. Hasalima a hirar tasa da Editar ta DW da ke Washington Ines Pohl Janar Hodges ya nunar da cewa, aikin kare Amirka sojojin ke yi, maimakon kallon da Shugaba Trump ke yi wa lamarin na cewar suna aiki ne na kare mutuncin Jamus. Amirkan dai ba ta sanar da ranar janye sojojin nata ba, sai dai sakataren tsaron nata Mark Esper ya ce ba za a bata wani lokaci ba, saboda wasu sauye-sauyen za su zo cikin makonni yayin kuma da wasu za su biyo daga bisani.