Amirka za ta naɗa jakadi a Somaliya | Labarai | DW | 03.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta naɗa jakadi a Somaliya

wani babban jami'in diplomasiya na Amirka ya ce shugaba Barack Obama zai naɗa sabon jakadina nan gaba.

Wannan shi ne karo na farko da Amirka za ta naɗa wani jakadin a Somaliya a cikin shekaru 20 bayan da ƙasar ta yi fama da yaƙi. Amirka ta rufe ofishin jakadancinta da ke a birnin Mogadishu tun a shekarun 1991 a lokacin faɗuwar gwamnatin mulkin kama karya ta Mohammed Siad Barre.

An shirya a gaba shugaba Obama zai bayyana sanarwa ta tabbatar da naɗa jakadin wanda zai kasance da zama a birnin Nairobi na Kenya. Amirka wacce ta ƙaddamar da yaƙi a Somaliya a ƙarƙashin wani shinrin na MDD daga shekarun 1992 zuwa 1995. Har yanzu tana tunawa da yaƙin uku ga watan Oktoba wanda a cikinsa masu kishin addini, suka kakapo jiragen yaƙinta na sama guda byu tare da kashe sojinta guda 18. Waɗanda wasu daga cikin gawarwakin sojojin aka riƙa jansu a ƙasa a kan tittunan birnin Mogadishu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal