Amirka za ta kara sojojinta a Nijar | Labarai | DW | 24.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta kara sojojinta a Nijar

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon za ta karfafa matakan tsaro ta hanyar kara jibge wasu dakarunta a kan iyakar kasashen Nijar da Mali, da zummar tallafa wa jamai'an tsaron kasar yakar masu haifar da barazanar tsaro.

Wannan mataki na Amirka na zuwa ne kwanani kalilan bayan wasu jerin hare-haren kwantan bauna da wasu 'yan bindiga suka kai kan iyakar Nijar da Mali, inda suka kashe dakarun Amirka hudu tare da wasu sojojin Nijar a farkon watan Oktoba.

A yanzu dai Pentagon na shirin girke karin wasu dakaru 800 a Nijar da wasu sauran kasashen Afirka, da nufin murkushe ayyukan ta'addancin kungiyar IS da ke zama karfen kafa a wasu kasashe da ke gabashi da yammacin nahiyar ta Afirka baki daya.

DW.COM