1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta bai wa 'yan Venezuela mafaka

March 9, 2021

Amirka ta ce za ta bai wa dubban 'yan kasar Venezuela daman neman mafaka a kasarta, batun da ya yi hannun riga da dokokin tsohon shugaban kasar Donald Trump.

https://p.dw.com/p/3qNTx
Kolumbien Migration l Flüchtlinge aus Venezuela - Highway in Cucuta
Hoto: Schneyder Medoza/AFP/Getty Images

Za a bai wa wadanda ke gudun duk wata danniya ta siyasa ko matsin tattalin arziki izinin zama na wucin gadi a Amirkan.

Wani babban kusa a gwamnatin Biden ya baiyana cewa a kalla mutane dubu dari 3 ne za su ci gajiyar sabon tsarin. Duk da cewa tsohon shugaban kasar Donald Trump na goyon bayan shugaba Nicolas Maduro, ya ki bai wa 'yan Venezuela kariya saboda tsattsaurar ra'ayinsa kan baki.

Tun bayan hawa kan karagar mulki a watan Janairu 2021 shugaba Joe Biden ya sauya dokokin Trump da ya baiyana a matsayin manufofin rashin mutunta dan Adam.