1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta ba wa Turkiyya garkuwar hare -haren Siriya

December 14, 2012

Sakataren tsaron Amirka, Leon Panetta ya amince da ba da garkuwar makamai masu linzami sanfulin "Patriot" guda biyu ga kasar Turkiya

https://p.dw.com/p/172S8
Hoto: picture-alliance/dpa

Kamar dai yadda BBC ta rawaito sojojin Amirka guda 400 za su kula da aikin girke garkuwar da za a yi a karshen watan Janairu mai kamawa domin kare kasar Turkiyya da ke zaman mamba ta kungiyar NATO daga duk wani hari da Siriya za ta kai mata. Kasashen Jamus da Holland su kuma za su ba da garkuwa guda biyu da sojoji 400.

Ma'aikatar tsaron Jamus ita kuma za ta ba wa Turkiyya gakuwar makaman masu linzami guda biyu da kuma sojoji 400 domin kare kanta daga duk wani hari da za ta fuskanta daga Siriya. Hakan ta bayyana ne bayan da majalisar dokokinnJamus ta Bundestag ta yi na'am da wannan shiri bayan kada kuri'u 461 akan kuri'un rashin amincewa 86 domin taimaka wa Turkiyar wadda ta nemi wannan taimako daga kungiyar NATO . Gwamnatin Jamus t ace wannan shiri da zai gudana har ya zuwa watan Janairun shekarar 2014 zai ci sama da Euro miliyan 25. Hakan za ta ba da damar dora haramci tashi da saukar jiage akan Siriya ko kuma tura sojoji ´domin shiga yakin basasan kasar. Su dai na'urorin na kariya da Jamus za ta ba da su za a girke su ne a yankin kudu maso gabashin Turkiyar a tazarar kilimita 120 daga iyakar kasar da Siriya. Kasar Holland ita kuma za ta ba da garkuwa guda biyu

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Saleh Umar Saleh