Amirka taya shugaba Ouattara murnar sake zaben sa a Ivory Coast | Labarai | DW | 29.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka taya shugaba Ouattara murnar sake zaben sa a Ivory Coast

Yin zaben a gama lami lafiya ya nuna a fili irin banbancin da kasar ta samu idan aka kwatanta da shekarar 2010.

A ranar Alhamis din nan kasar Amirka ta taya shugaba Alassane Ouattara murnar sake nasara a zaben da aka yi a Ivory Coast abin da Amirka ta bayyana da cewa babbar nasara ce ga kasar.

Wannan nasara dai da shugaba Ouattara ya samu a zaben da aka yi a wannan kasa da Faransa ta yi wa mulkin mallaka a yammacin Afirka a karshen makon da ya gabata, yin zaben a gama lami lafiya ya nuna a fili irin banbancin da kasar ta samu idan aka kwatanta da shekarar 2010. A wancan zabe dai shugaba kasar na wancan lokaci Laurent Gbagbo yaki amincewa da shan kayi abin da ya jefa kasar cikin yanayi na tashin hankalin da ya jawo rasa rayukan mutane dubu uku.

A cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Amirka John Kirby al'ummar kasar ta Ivory Coast sun cancanci a yaba musu ya dda suka gudanar da zaben na ranar 25 ga watan Oktoba ba tare da wani tashin hankali ba.