Amirka tana nazarin matakan soja a Siriya | Siyasa | DW | 27.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amirka tana nazarin matakan soja a Siriya

Ƙasashen yamma sun bayyana imanin cewar gwamnatin Siriya ce ta ke da alhakin kai wa al'ummar ƙasar harin makamai masu guba tare da kashe darurruwan farar hula.

Bayan zargin da ake yiwa gwamnatin Siriya ta shugaba Bashar al-Assad da laifin amfani da makamai masu guba a yaƙin da 'yan tawaye, tare da haddasa mutuwar daruruwan farar hula a ƙasar, yanzu akwai alamun lokacin shawarwari ko tattaunawa ya wuce. Daruruwan mutane suka mutu, aƙalla 3000 suka sami rauni. Wannan dai shi ne sakamakon binciken da ƙungiyar likitocin duniya ta sanar, bayan zargin amfani da makamai masu guba a kusa da birnin Damascus a makon jiya a yaƙin ƙasar. Gwamnatocin ƙasshen yamma da dama sun yi imanin cewar shugaba Bashar al-Assad shine yake da alhakin amfani da makaman masu guba.

To musamman ga Amirka, daraja da mutuncinta zasu dogara ne ga irin martanin da zata mayar, saboda tun a watannin baya shugaba Barack Obama yace da zaran gwamnatin ta Siriya tayi amfani da makamai masu guba, to kuwa ba za'a kyale ta zauna lafiya ba. Tun da kuwa yanzu ana zargin tayi hakan, wajibi ne ta sa ran kasashen yama zasu saukar mata da karfin makamai. Majiyoyin tsaro a Amerika sun nunar da cewar yanzu shugabanni a Washington suna nazarin matakan da za su iya ɗauka.

Syrien Präsident Assad Ansprache Rede Damaskus 04.08.2013

Shugaban Siriya Bashar al-Assad

Zaɓi na farko shi ne Amirka ta ware wani yanki tsaro. Hakan yana nufin za'a haramtawa jiragen saman yaƙi ko masu saukar ungulu na gwamnatin Siriya su shiga sararin samaniyar wannan yanki, abin da zai hana shugaba Assad samun damar kai wa 'yan tawayen na Siriya hare-hare ta sararin samaniya. Hakan dai zai zama babban taimako ga yan tawayen, inji Hans-Joachim Schmidt, daga cibiyar nazarin zaman lafiya da sulhunta rikice-rikice ta Hessen.

"Yace yin haka zai zama babban taimako da goyon baya ga yan tawayen, saboda shugaba Assad ba zai kasance da wata dama ta kai wa 'yan tawayen hari da jiragen saman yaƙi ko masu saukar ungulu ba. Wato a taƙaice 'yan tawayen za su amfana daga wannan mataki."

To sai dai kafin yin haka, wajibi ne da farko Amirka ta lalata rundunar sojan sama ta Siriya, kamar yadda Paul Rogers, masani a fannin tsaro a cibiyar Oxford ya nunar. Yin haka zai zama abu mai matukar tsada, kuma musamman mai matukar haɗari, saboda Rasha ta yiwa Siriya alkawarin bata manyan makamai na zamani na tsaron sararin samaniya. Idan kuwa har Rasha ta cika wannan alkawari ta bai wa Siriya makaman, Amirka za ta kasance da gagarumar matsala a hannunta, inji masanin hanyoyin samun zaman lafiya, Hans- Joachim Schmidt. Saboda haka ne masanin yace baya zaton Amirka zata zabi wannan hanya, domin yin haka zai tsunduma Amir ikawan sosai a wannan rikici, abin da Amirkawan ba sa so. Bugu da ƙari kuma, kafin a kirkiro wannan yanki, sai an sami izinin hakan daga kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda China da Rasha babu shakka zasu hau kujerar naki.

Zaɓi na biyu shi ne amfani da rokoki, inda Amirkan take iya kai hare-hare domin lalata filayen saukar jiragen sama da sansanoni domin raunana sojan ƙasar ta Siriya. Tun da kuma mahukunta a Washington ba sa son shigar da ƙasarsu sosai a wannan rikici, hanya mafi dacewa ita ce kai wa Syria kwarkwaryar hare-hare ta amfani da jiragen saman yaki.

USA verstärken Marine-Präsenz vor syrischer Küste

Jiragen ruwan yakin Amirka kan hanyar zuwa gabar tekun Siriya

Hanya ta uku ita ce ta bai wa 'yan tawayen Syria makamai. Yanzu dai a hukumance Amirka kayan magunguna kawai take bai wa 'yan tawayen amma ba makamai ba, ko da shike ana sane da cewar 'yan tawayen suna samun makamai a zahiri ta hannun Turkiya da Jordan, wadanda Saudi Arabiya da daulolin yankin Gulf suka biya.

Wani al'amarin da ke iya tashi daga rikicin na Siriya da shisshigin ƙasashen yamma shi ne tsoma baklin ƙungiyoyin musulmi masu matsanancin ra'ayi a wannan rikici. Masanin hanyoyin zaman lafiya Hans-Joachim Schmidt ya nunar da cewar:

"Ƙasar Iran alal misali, tana iya jan hankalin irin waɗannan ƙungiyoyi, musaman Hisbollah su ƙara tsananta aiyukan su a yankin, misali a Lebanon, ko kuma Amirkan ta sami ƙarin matsaloli a Afghanistan, idan Iran ɗin ta kara goyon baya da taimakonta ga yan Taliban. Saboda haka shisshigin Amirkan a Siriya yana iya zama sanadin kara danyacewar mummunan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya."

Bisa la'akari da waɗannan matsaloli ne ya sanya Amirka har yanzu ta ke taka tsan-tsan a game da yiwuwar shigar da kanta da ƙarfin soja a rikicin na Siriya. Maimakon haka, Amirkan tana iya sabon yunƙuri ta hanyar diplomasiya, tare da barazanar cewar idan aka sake samun amfani da makamai masu guba a Siriya, za ta shiga da ƙarfinta na makamai a ƙasar.

Mawallafi: Hartlep/Umaru Aliyu
Abdourrahamane Hassane