1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya na shirin kai hari kan Kurdawa

Abdourahamane Hassane
January 14, 2019

Shugaban Amirka Donald Trump ya yi gargadin cewar Turkiyya za ta iya shiga cikin wadin tsaka mai wuya a fuskar tattalin arziki inda har ta kuskura ta kai hari a kan Kurdawa a yankin arewacin Siriya.

https://p.dw.com/p/3BUxU
G20 Gipfel in Hamburg | Erdogan & Trump
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/Turkish Presidency

Donald Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na Twitter cewar al'amuran tattalin arziki na Turkiyya za su dagule idan har ta kai harin sannan kuma ya yi kira ga Kurdawa da su guji yin tsokana da farko. Shugaba Recep Tayyip Erdogan dai na Turkiyya ya yi shelar kai wani sabon hari a kan mayakan sa kai na Kurdawan. A cikin watan Disambar da ya gabata ne dai shugaban na Amirka ya ba da sanarwa cewar kasarsa za ta janye sojojinta daga Siriya.

´