Amirka ta yi barazana ga Rasha kan Aleppo | Labarai | DW | 28.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yi barazana ga Rasha kan Aleppo

Amirka ta yi barazanar cewa za ta tsaida duk wata hulda da Rasha a neman warware yakin da Siriya ta fada sama da shekaru biyar.

A ranar Laraban nan sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yi barazana ta kawo karshen duk wani aikin hadin kai da ke wakana tsakanin Amirka da Rasha a kokari na kawo karshen yakin basasar Siriya muddin Rasha da gwamnatin Siriya su ka gaza tsaida lugudan wutar da ke wakana a Aleppo. Fiye da mutane 250 ne dai ake fargabar sun halaka tun daga makon jiya bayan komawa ruwa na barin wuta a wannan birni da aka yi wa kawanya.

Wannan gargadi na Mista Kerry da ke zuwa ta wayar tarho a ranar  Laraban nan ya kira takwaransa na Rasha Sergey Lavrov inda ya yi wannan barazana a wannan yakin na Siriya da ya kwashe shekaru biyar da rabi ana fafatawa. An dai dade ana ruwa kasa na shanyewa ganin wannan ba shi ne karon farko ba, a irin wannan gargadi ciki kuwa har da barazana  da Shugaba Obama ya yi cewa Amirka za ta dauki mataki na soji idan har gwamnatin Shugaba Bashar Assad ta yi amfani da makami mai guba a yakin da take yi da 'yan tawaye.