Amirka ta yi Allah wadai da kisan jaririn Falasdinawa | Labarai | DW | 31.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yi Allah wadai da kisan jaririn Falasdinawa

Wannan dan jariri dai ya rasu ne bayan kunar da ya sha cikin ayyukan ta'addancin na Yahudawa masu tsatstsauran ra'ayi bayan sanya wuta a gidajen wasu Falasdinawa biyu.

Palästina Trauerfeier für das getötete Baby in Duma bei Nablus

Jana'izar jaririn Falatsinawa

Gwamnatin shugaba Barack Obama ta yi Allah wadai da kisan wani jariri Bafalasdine da ake zargin wasu Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi da aikatawa a yamma da kogin Jordan bayan da suka banka wuta a gidan da jariri yake ciki.

Gwamnatin Amirka dai ta bayyana kisan a matsayin kisa na rashin imani wanda ke bukatar ganin an hukunta wadanda suka aikata shi.

A wani jawabi da ofishin harkokin wajen Amirka ya fitar a ranar Juma'an nan ya yaba da yadda Firaminista Benjamin Netanyahu ya fito ya yi kakkausan suka da wannan mugun aiki inda ta bukaci mahukuntan na Isra'ila su yi duk mai yiwuwa wajen ganin wadanda suka aikata kisan jaririn sun gurfana a gaban shari'a.

Har ila yau ofishin harkokin wajen na Amirka ya bukaci dukkanin bangarorin biyu su kwantar da hankula kada wannan batu ya tada tsohon rikici da ke tsakanin bangarorin.

Wannan dan jariri dai ya rasu ne bayan kunar da ya sha cikin ayyukan ta'addancin na Yahudawan bayan da suka sanya wuta gidajen wasu Falasdinawa biyu da sanyin safiyar Juma'an nan, lamarin da ya sanya bayan jaririn yayansa dan shekaru hudu da iyayensu suka sami raunika.