Amirka ta tsaida yaki da ta′addanci a Yemen | Labarai | DW | 24.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta tsaida yaki da ta'addanci a Yemen

Cikin ayyukan da Amirka ke shirin tsaidawa har da daina kai farmaki ta hanyar amfani da jiragen sama masu sarrafa kansu da kansu na wani lokaci a fadin kasar Yemen.

Kasar Amirka ta tsayarda wasu ayyuka da take yi na taka birki ga mayakan Kungiyar Al-ka'ida a Yemen, bayan da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran suka kwace ikon kasar. Bayanin hakan ya fitowa ne daga wasu jami'an gwamnatin kasar ta Amirka a Washington.

Koma bayan da kasar ta Yemen da ke samun goyon bayan Amirka ta samu, ya sanya koma bayan ayyukan ita ma kasar ta Amirka na yaki da ta'addanci a cewar wasu jami'an tsaron na Amirka. Suka ce wannan ba karamin koma baya bane ga ayyukan na mahukuntan birnin Washington a yakin da take yi da mayakan Alka'ida da ke a yankin mashigar tekun Arabiya wacce ke zama kashin bayan rassan kungiyoyin masu fafutika da makamai.

A cewar wasu jami'ai uku na Amirkan, cikin ayyukan da aka tsaida har da daina kai farmaki ta hanyar amfani da jiragen sama masu sarrafa kansu na dan wani lokaci, bayan da shugaban kasa da Firaminista da ma mambobin majalisar zartarwa suka bayyana ajiye mukamansu, abin da ke nuna barazana ta yiwuwar tunkarar fadawa yakin basasa da kasar ka iya ruftawa.