1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta soma aiki da sabon haraji kan Chaina

Gazali Abdou Tasawa
August 23, 2018

Kasar Amirka ta soma a wannan Alhamis aiwatar da matakin dora sabbin harajin kwastam na kaso 25 daga cikin dari kan wasu kayayyakin kasar Chaina da ake shigo da su a kasar.

https://p.dw.com/p/33c90
Symbolbild China - USA Strafzölle | getrocknete Früchte aus den USA
Hoto: picture alliance/dpa/Xu Congjun

Da wannan sabon karin haraji wanda ya kai na miliyan dubu 16 na Dalar Amirka, kasar ta Amirka ta dora a jumulce harajin miliyan dubu 50 na Dalar Amirka kan hajojin kasar ta Chaina da ke shigowa kasar. 

Sai dai kuma jim kadan bayan da Amirka ta soma aiki da wannan mataki ita ma kasar ta Chaina ta mayar da martani ta hanyar dora sabon harajin fito na kimanin Dalar Amirka miliyan dubu 16 kan hajojin kaar ta Amirka da ke shiga kasarta.

A karkashin wannan takun saka dai kasar ta Amirka ta yi barazanar yiwuwar kara dora wani sabon harajin na kimanin miliyan dubu 200 na Dalar Amirka kan hajojin kasar ta Chaina a watan Satumba mai zuwa. 

Shugaba Donald Trump ya dauki wannan mataki ne kan kasar ta Chaina da nufin ladabtar da ita a bisa zargin da yake yi mata na ha'intar kasarsa a cikin huldar kasuwancin da ta hada kasashen nasu. 

Wannan mataki na Amirka na zuwa ne a daidai lokacin da a wannan Alhamis wakillan kasashen biyu suka shiga kwana na biyu na tattaunawar a birnin Washington da nufin gano bakin zaren warware matsalar.