1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta sha alawashin kashe kwayar cutar Ebola

Pinado Abdu WabaOctober 3, 2014

Cutar Ebola ta je Amirka ta hanyar wani dan Liberiya mai dauke da ita amma mahukuntan kasar sun ce sun riga sun dauki matakan da za su dakile ta tun bata yi nisa ba

https://p.dw.com/p/1DPZW
Pressekonferenz zu Ebola-Patient
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Rumpenhorst

A sharhin da ta rubuta jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce da ma lokaci ne kawai ake jira kafin cutar wadda ta yi watanni tara tana yaduwa yanzu ta kaura daga nahiyar Afirka bayan da a ranar 20 ga watana satumba wani dan Laberiya ya kai cutar Jihar Texas a Amirka, inda a yanzu haka ya ke jinya a wani asibiti da ke birnin Dallas. A wani taron manema labarai da cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amirkan ta yi, daraktan cibiyar Thomas Frieden ya yi kokarin kwantar da hankular 'yan kasar.

Ita ma Jaridar Tagesspiegel wadda ta dauki wannan labarin ta bayyana yadda Thomas Frieden ya ce Amirka ta babanta da Afirka dan haka matakan da za su dauka ma sun banbanta kuma babu shakka za su dakatar da yaduwar wannan cuta. Matakan da cibiyar za ta dauka masu sauki ne, kwararru wajen gano kwayar cuta za su nemo duk wadanda suka hadu da wannan mutumi, bayan da alamun cutar suka bayyana a jikinsa, sannan su kebe su na tsawon kwanaki 21, lokacin da zasu rika bincika su dan ganin ko su ma za su nuna alamun kamuwa da wannan cutar, a dalilin haka yanzu an samar da wata taswira, wadda za ta nuna duk inda ya shiga tun daga sadda jirginsa ya isa kasar. Asibitin Texas Health Presbyterian dai inda wannan mutumi ke samun kulawa ta ce dama a shirye take wa irin wannan cuta amma kuma dole ne za a gudanar mata da bincike tunda a ranar 26 ga watan Satumba ya je wurin dan samun magunguna amma kuma aka tura shi gida, sannana kuma bayan kawanki hudu aka same shi da alamun cutar.

Ebola Patient in die Uni-Klinik Frankfurt eingeliefert 03.10.2014
Yaduwar Ebola sai da karin matakaiHoto: Reuters/R. Orlowski

Shekara ta zagayo tun hatsarin jirgin ruwan masu gudun hijira a Lampedusa

Ita kuwa mujallar Die Zeit, ta yi labarin cika shekara guda da afkuwar hatsarin jirgin ruwan nan na Lempadusa inda 'yan gudun hijira 387 suka hallaka, inda ta zanta da wasu daga cikin wadanda suka rayu bayan wannan hatsari, kamar wani mutumi mai suna Fistum, dan asalin Eritrea, wanda ya ce har yanzu a kusan kowani dare, ya kan farka cikin firgita, da dimuwa saboda ya yi mafarkin cewa ya fada cikin ruwa kuma shi da sauran jama'a na kokarin tsira da rayuwarsu. Ya tsallaka rijiya da baya a wannan rikicin da ya ja hankalin duniya ya kuma yi tasiri kan wasu manufofin siyasar samar da mafaka. Jaridar dai ta cigaba da labarin Fistum wanda ya bar gida in banda gorar ruwa babu ko kudi a jikinsa. Ya ce duk wani karfin iko na kasar ta sa ta Eritriya shugaba Isaya Afewrki ke rike da shi, shugaban wanda ya kasance gwarzon gwagwarmayar neman 'yanci, ya karya alkawarin da yayi na girka mulkin demokradiyya a kasar bayan da suka shafe shekaru talatin suna yakin basasa

Symbolbild Flüchtlinge Mittelmeer Bootsflüchtlinge Migranten
Har yanzu baki na kwarara a LampedusaHoto: picture-alliance/dpa

Joseph Kabila na Kwango ya bar 'yan kasarsa a duhu

Hatta wasu yankunan yankin gabashin Jamhuriyra Demokradiyyar Kwango sun fara kasancewa cikin kwanciyar hankali amma kuma 'yan kasa da shugabansu Joseph Kabila na cigaba da kasancewa tamkar bakin da basu fahimci juna ba. Wannan shi ne abin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bayyana, ta ce shugaba Joseph Kabila ba ya magana kuma wannan ce matsalar, yanzu an watanni shidda ke nan al'ummar na hasashen matakin da zai dauka nan gaba ko zai sauya kundin tsarin mulkin kasar ne ya cigaba da kasancewa shugaba ko ko a a. A hukumance kamata ya yi ya sauka daga kujerara mulkin kasar bayan wa'adi biyu sai dai 'yan adawa sun yi ammananr hakan ba zai faru ba. Duk sadda ya je MDD zai karanto jawabin da ke cewa za a yi zabe amma kuma kawo yanzu an dage zaben kananan hukumomi da na majalisar dokoki da na wakilai da na larduna zuwa shekara mai zuwa. To sai dai akwai abokan hammaya da ke hankoran kalubalantar shugaban mai mulki a zabuka masu zuwa. To karshen sharhin jaridun na Jamus ke nan a kan nahiyar Afirka

Joseph Kabila Kabange 25.09.2013
Joseph kabila shuguban kasar KwangoHoto: picture-alliance/dpa