Amirka ta samu damar yi wa Assange shari′a | Labarai | DW | 10.12.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta samu damar yi wa Assange shari'a

Gwamnatin Amirka ta yi nasarar daukaka kara kan hukuncin da wata kotun Birtaniya ta yanke na hana mika mutumin da ya kafa WikiLeaks Julian Assange daga Birtaniya.

Bilder der Woche KW 48 Flash-Galerie 1

Washington ta kalubalanci shawarar da aka yanke a watan Janairu cewa Assange dan Australia mai shekaru 50, ya yi barazanar kashe kansa idan aka maida shari'ar da ake masa zuwa Amirka.

Gwamnatin Amirka na son Assange ya fuskanci shari'a kan wallafar da Wikileaks ta yi shekarar 2010 na wasu bayanan sirri na soja da ya shafi yakin Amirka a Afghanistan da Iraki.