Amirka ta rugaza asibiti a Afganistan | Labarai | DW | 03.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta rugaza asibiti a Afganistan

Akalla fararen hula tara suka mutu wasu dadama suka jikkata bayan farmakin jiragen sama da aka kai a asibitin Kunduz yayin da masu jinya ke barci.

Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa farmakin da sojojin Amirka suka kai har sau hudu ya lalata asibitin kungiyar bada agaji ta Doctors Without Boarders. Harin dai a cewar rudunar tsaron NATO wanda ta zargi Amirkawa da kaiwa, an kai shi ne cikin dare kimanin karfe uku na dare agogon Afganistan lokacin da marasa lafiya ke barci. Yanzu haka dai kungiyar Doctors Without Boarders ta ce ana ci gaba da zakulo wadanda ke da rai yayin da wasu kuwa suka bace ba a kai ga gano inda suke ba. Kungiyar ta yi Allah wadai da farmakin na sojan Amirka domin asibitin shi ne daya tilo da aka dogara da shi wajen samar da jinya ga al'ummar yankin da yaki ya dai-daita. A cewar hukumomin yankin an dau sama da mintuna 30 ana luguden wuta kan asibitin duk kuwa da bayan an fada wa Amirkawan cewa, wannan asibiti ne ba sansanin makiya ba ne.