Amirka ta rufe ofishin Jakadancin ta da ke kasar Turkiyya | Labarai | DW | 05.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta rufe ofishin Jakadancin ta da ke kasar Turkiyya

Kasar Amirka ta sanar ta rufe ofishin jakadancinta da ke birnin Ankara na kasar Turkiyya sakamakon samun rahoton barazanar kai hari ofishin da kasar ta ce ta samu a ranar Lahadi.

A halin yanzu mahukunta a Turkiyya sun dauki tsauraran matakan tsaro tare da shawartar jama'a a kan su guji harabar ofishin jakadancin Amirka da kuma dukkan guraren da 'yan Amirka suke gudanar da harkokin su na yau da kullum a fadin kasar ta Turkiyya.

A wani cigaban kuma ofishin jakadancin na Amirka ya sanar da soke ganawa da masu neman izinin shiga kasa wato bisa da kuma gudanar da dukkanin ayyuka a ofishin har zuwa lokacin da Amirka za ta gamsu da ingantuwar tsaro.