Amirka ta nuna takaici da garkuwa da ′yan mata a Najeriya | Labarai | DW | 10.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta nuna takaici da garkuwa da 'yan mata a Najeriya

Matar shugaban Amirka ta yi tir da garkuwa da 'yan mata 'yan makaranta da 'yan Boko Haram suka yi a yankin arewa maso gabacin Najeriya.

Uwargidan shugaban Amirka Michelle Obama ta gabatar da jawabin mako-mako da ake watsawa ta radiyo, a madadin Shugaba Barack Obama, inda ta nuna matukar fusata da garkuwa da 'yan mata fiye da 200 a wata makaranta ta Najeriya.

Sannan ta ce a kamar sauran miliyoyin mutanen duniya suna cike da bakin rai na faruwar lamarin, wanda ta kara da cewa babu makawa aikin ta'addanci ne.

Kwararrun jami'an tsaron kasashen Amirka da Birtaniya sun isa Najeriya inda suka shiga aikin neman ceto 'yan mata 'yan makaranta sama da 200 da 'yan kungiyar Boko Haram suke garkuwa da su, bayan kwashe 'yan matan daga makarantar garin Chibok na Jihar Borno. Kungiyar ta Boko Haram mai kaifin kishin addinin Islama ta tabbatar da garkuwa da 'yan matan, inda shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya yi barazanar sayar da su. Rundunar sojin Najeriya ta musanta sakaci kan sace 'yan matan.

Birtaniya ta ce tana burin kwato 'yan matan da dakile kungiyar ta Boko Haram baki daya. Kasashen China, da Faransa da kuma Spain duk sun yi alkawarin ba da taimako. Ana ci gaba da zanga-zanga a ciki da wajen kasar tare da nuna bacin rai kan yadda aka sace 'yan matan.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal