Amirka ta nuna aniyar sauyin alkibla a rikicin Siriya | Labarai | DW | 28.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta nuna aniyar sauyin alkibla a rikicin Siriya

Amirka ta tabbatar cewa an aika wa Iran goron gaiyata zuwa taron tattaunawa a birnin Vienna don neman mafita a yakin basasan kasar Siriya.

USA Verteidigungsminister Ashton Carter

Sakataren tsaron Amirka Ashton Carter

Kasar Amirka ta nuna shirin sauyin alkibla a rikicin kasar Siriya. Yanzu haka sakataren tsaron Amirka Ashton Carter ya ce a shirye kasarsa take ta yi amfani da sojojinta na kasa a yakin da take yi da kungiyar IS a Siriya. Ya ce Amirka ba za ta ja da baya ba wajen tallafa wa abokanninta su kai hari ta kasa kan IS ko ma ita da kanta ta jagoranci kai irin wannan hari ko ta kasa ko ta sama. Bugu da kari sabanin manufarta a da, yanzu Amirka na son ta tattauna da Iran game da rikicin kasar Siriyar. Ashton Carter ya ce suna da niyyar gayyatar Iran zuwa taron da za a yi a birnin Vienna. A martanin da ta mayar gwamnatin Iran ta ce za ta tura wakili a taron da zai gudana a birnin na Vienna.